A karon fakro, shugaban rundunar RSF a Sudan ya amince da cewa dakarunsa sun yi rasa birnin Wad Madani ga rundunar sojin ƙasar da suke yaƙa, a wani koma-baya mafi girma da rundunarsa ta fuskanta tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar.
A cikin wani sakon murya, an ji Janar Mohamed Hamdan Dagalo, na magana cikin fushi da takaici, yana lasar takobin ci gaba da yaƙi ko nan da zuwa shekara 20 ne.
”A yau mun yi rashin nasara a filin daga, amma ba mu yi nasara a wannan yaƙi ba, watanni 21 kenan muna yakar sojin Sudan, don haka za mu ci gaba da yaƙarsu ko da nan da shekara 21 ne”, in ji Janar Dagalo.
Ya ƙara da cewa sojojin Sudan yi nasara ne saboda ƙarfinsu a sama, da kuma jirage marasa matuƙan da Iran ke ba su.
An yi ta gudanar da bukukuwa a wasu sassa daban-daban na Sudan bayan da sojoji suka sanar da kwace birnin.