Mayakan kungiyar Houthi dake ƙasar Yemen ta ce sun kai hari da makamai masu linzami biyu a filin jirgin saman Isra’ila, awanni bayan rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kakkaɓo wani makami da suka harba mata.
“Makami na farko (da aka harba) ya nufi Filin Jirgin Saman Ben Gurion Airport” aTel Aviv, yayin da makami na biyu ya nufi wata tashar samar da hasken lantarki da ke kudancin Birnin Ƙudus, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar Houthi ta fitar.
Kazalika ƙungiyar ta ce ta kai hari kan babban jirgin ruwan Amurka mai suna USS Harry S. Truman wanda ke ɗaukar jiragen sama.
Kawo yanzu rundunar sojin Amurka ba ta ce komai kan wannan ikirari ba.