Akwai yiwuwar a sabuwar shekarar 2025 kamfanonin sadarwa a Najeriya su samu amincewar hukumar da ke kula da harkokin sadarwa NCC domin su ƙara kuɗin kiran waya da na data.
Wani babban jami’i wandada ya buƙaci a sakaya sunanshi ya ce hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ka iya bai wa kamfanonin damar ƙara kuɗin.
Rahotanni sun ce duk da tsadar rayuwa amma anƙi amincewa kamfanonin su ƙara kuɗin kira sama da shekaru 11 da suka gabata.
Kamfanoni kamar MTN da Airtel da 9Mobile sun jima suna miƙa buƙatar ƙarin kuɗin ga Hukumar duba da yanayin tattalin arziki a ƙasar.
Wasu majiyoyin kamfanonin sadarwar sun ce ƙarin da za a fuskanta a ƙasar zai iya kaiwa kaso 40.
Wannan na nufin cewa kiran waya na minti 1 zai tashi daga naira 11 zuwa 15.40, aika sakon kar ta kwana a salula zai tashi daga naira 4 zuwa naira 5.60.
Farashin data 1GB zai tashi daga naira dubu 1 zuwa dubu1 da 400.