Shugaban hukumar Alhaza Najeriya NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce yanzu haka hukumar ta na cigaba da kai ziyara jihohi da wajan wasu masu ruwa tsaki a faɗin ƙasar ne domin ƙarfafa shirye-shiryen da hukumar ke yi na tsara aikin Hajjin da ya dace a 2025 da kuma bayanta.
Farfesa Abdullahi Saleh ya bayyana hakan ne ranar Juma’a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris a gidan gwamnatin jihar dake Birnin Kebbi.
Farfesa Pakistan ya lissafo wasu sabbin matakai da hukumarsa ke ɗauka domin ragewa alhazai raɗaɗi a gida da kuma ƙasar Saudi Arabia.
A cewarsa, matakan sun haɗa da yin tunani domin biyan kuɗin aikin Hajji a Naira maimakon dalar Amurka, yana mai cewa, “wannan shi ne zai rage farashin ƙuɗin da ake biya.
Saleh ta yaba da irin goyon bayan da Dr Idris ke ba shi wajen ganin an samu nasarar aikin Hajjin 2025.
“Tare da goyon bayanku da sauran masu ruwa da tsaki, mun himmatu sosai wajen ganin mun kawar da wannan mummunar dabi’a da muka gada a NAHCON.”
Lokacin da yake jawabin, Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris, ya buƙaci hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ɗauki ƙwararan matakai domin inganta ayyukan hajjin 2025.
Gwamnan ya ce ya tuna da irin ƙalubale iri daban-daban da suka kawo cikas wajen gudanar da ayyukan Hajji na shekarar 2024 da NAHCON ta jagoranta.
Acewar gwamnan ya tuno da irin rashin kyakkyawan shiri da aka yi musamman wajan samar da masauki ga maniyyata da sauran muhimman ayyuka.
Har ilayau ya koka da yadda hukumar ba ta yi jigilar maniyyata yadda ya kamata ba a Makkah da Madina da sauran wurare masu tsarki.
“Ni ma shaida ne a lokacin da na yi aikin Hajjin karshe da kaina tare da wasu gwamnoni da wasu manyan ‘yan Najeriya da alhazanmu suka maƙale aka bar su suna shan wahala” Inji Gwamna Nasir Idris
Dr. Idris ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2025 mai inganci.
“Za mu ci gaba da bayar da tallafin da ake buƙata ga hukumar jin daɗin Alhazai (PWA) da kuma NAHCON ta wannan hanyar kuma ba za mu taɓa yin ƙasa a gwiwa ba,” inji shi.
Shugaban hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi (PWA), Alhaji Faruk Musa Yero Enabo ya yabawa Dakta Idris bisa yadda ya sanya jihar Kebbi ta zama abin koyi wajen gudanar da ayyukan Hajji a Nigeria.
Ya ce zaɓin da jihar ta yi na ƙaddamar da ziyarar a yankin Arewa maso Yamma ya nuna yadda Dakta Idris ke ci gaba da tallafa wa hukumar sa da kuma ta NAHCON.
Shugaban ya danganta jerin gaggarumin ci gaba da hukumar ta samu da goyon baya da jajircewar Gwamnan.
Ya ƙara da cewa dukkan mahajkatan 2024 kowannensu ya karɓi kudadensa na Naira 61,080, inda gwamnatin jihar ta yi watsi da cajin bankuna daban-daban kamar yadda Dakta Idris ya umarta.