Matatar mai ta Dangote ta sanar da karya farashin litar man fetur zuwa 899.50
Mai magana da yawun rukunin Kamfanonin Dangote Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar yau Alhamis.
Inda ya ce an rage farashin fetur daga N970 zuwa N899.50 domin mutane su samu sauƙin tafiye-tafiye a lokutan bukukuwan ƙarshen shekara.
A watan Nuwambar da ya gabata ma, matatar man mai zaman kanta a Najeriya ta rage farashin litar man zuwa naira 970.
Chiejina ya ƙara da cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama’ar Najeriya man fetir mai inganci kuma cikin farashi mai sauƙi.
Acewarsa “Domin samar da sauƙi kan harkokin sufuri a lokacin hutun ƙarshen shekara, matatar mai ta Dangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashi. Daga yau za a riƙa sayar da man a kan naira 899.50 kan kowacce lita, daga mtatar man tamu.”