NBS ta ce an biya kuɗaɗen fansar ne tsakanin watan Mayu na shekarar 2023 zuwa watan Afrilun shekarar 2024.
Rahoton ya ƙara da cewa kashi 65 cikin 100 na gidajen da iftila’in garkuwa da mutane ya shafa sun biya kuɗin fansa domin a saki ‘yan’uwansu.
A rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata game da laifuka da kuma yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a Nijeriya, ta ce masu garkuwa da mutane sun kashe fiye da mutum 600,000 sannan suka sace fiye da mutum miliyan biyu a faɗin Nijeriya tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
“Matsaƙaicin kuɗin fansar da aka biya ya kai N2,670,693, yayin da jumullar kuɗin fansar da aka biya a lokacin ya kai N2,231,772,563,507,” kamar yadda rahoton NBS ya bayyana.
Rahoton ya ce garkuwa da mutane da aka yi a faɗin ƙasar ya kai 2,235,954 inda aka yi garkuwa da mutane sau 1,668,104 a karkara fiye da cikin birane inda aka yi sau 567,850.
“Idan aka yi la’akari da shiyyoyin da garkuwa da mutanen ya fi faruwa kuwa, za a ga cewa yankin arewa maso yammacin Nijeriya ne ya fi yawan garkuwa da mutane (1,420,307), inda arewa maso tsakiyar Nijeriya yake binsa (317,837), sannan kuma kudu maso gabashin Nijeriya ne na ƙarshe (110,432),” in ji hukumar.
Cikin iyalan da suka fuskanci garkuwa da mutane, rahoton ya nuna cewa kashi 80.5 cikin 100 sun sanar da ‘yan sanda.
“Shiyyar kudu masu kudun Nijeriya ce mutane suka fi sanar da mjutane cewa an yi garkuwa da ‘yan uwansu inda kashi 100 cikin 100 na wadanda abin ya shafa suka sanar da ‘yan sanda, yayin da shiyyar arewa maso tsakiyar Nijeriya ke binta da kashi 89.6 cikin 100 suka sanar da ‘yan sanda kuma arewa maso yammmacin Nijeriya ta zo ta ƙarshe inda kashi 73.9 cikin 100 suka sanar da ‘yan sanda,” kamar yadda rahoton ya bayyana.
“Idan kuma aka yi la’akari da inda mutane ke zaune kuma birane sun fi sanar da ‘yan sanda inda suka samu kashi 87.1 cikin 100 yayin da mutanen ƙauyuka suka sami kashi 77.3 cikin 100.”
Rahoton ya ƙara da cewa an kashe wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin yayin da aka sake wasu daga cikinsu.
Ya nuna cewa daga cikin mutanen da aka ba da labarin cewa an yi garkuwa da su, an sake kashi 82.1 cikin 100, inda ka kashe kashi 12.8 cikin 100 yayin da har yanzu kashi 3.3 cikin 100 suna hannun masu garkuwa da mutane.