Ana zargin wani matashi dan shekara 22 mai suna Godwin daga yankin Elebele a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa da cakawa mahaifiyarsa wuka bayan ya gaza samun nasarar amfani da ita wajen yin tsafi.
A cewar wasu majiyoyi, mutumin da ake zargin ya dawo garin ne makonni kalilan da suka wuce bayan ya yi bulaguro na tsawon watanni a makwabciyar jihar inda ya je wajen wata matattara ta ‘yan Yahoo da ake kira da HK.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban kungiyar matasa na kauyen Elebele, Kwamared Precious Okala, ya shaida wa manema labarai cewa an kira shi da misaln karfe 6 na yammacin ranar da lamarin ya afku inda daga zuwansa wajen ya tarar da gawar wata mace kwance cikin jini da kuma danta nata wanda matasan garin suka daurewa hannu a gefe.
Ya ce, ” Makwabtan yaron sun ce sun ji ana ta kai ruwa rana a ranar da zai aikata ta’asar inda dadabniya ta yi yawa tsakaninsa da mahaifiyar tasa daga bisani kuma suka ji shiru ashe ya caka mata wuka ne a cikinta lamarin da ya yi ajalinta.
A bangare guda kuma, an mika mutumin da ake zargin zuwa ga rundunar ‘yan sandan jihar ta Bayelsa.
Mai magana da yawun rundunar, Musa Mohammed, ya ce an mika lamarin ga hannun sashen binciken manyan laifuka na jihar don gudanar da cikakken bincike.