Kwamitin Musamman na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce hanyoyin yakin da Isra’ila ke bi a Gaza daidai suke da kisan kare dangi, ciki har da kisan fararen hula da ake yi da kuma wahalar da Falasdinawa.
Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya afka wa yankunan kudancin babban birnin kasar Labanon bayan da Isra’ila ta gargadi mazauna yankin su fice daga wani bangare na sansanin Hezbollah, kamar yadda hotunan AFP suka nuna.
Wani hayaki mai launin toka ya turnuƙe yankin bayan harin na baya-bayan nan tun bayan da Isra’ila ta tsananta kai hare-haren bam a Lebanon a watan Satumba.
Jim kadan gabanin harin, Isra’ila ta yi gargadi ga mazauna yankin da su bar gidajensu.
Harin bama bamai da Isra’ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan da ke birnin Gaza inda fararen hula ke zaune, ya hallaka Falasdinawa akalla uku.
A wani hari na daban da aka kai a wajen makarantar Hamama, Isra’ila ta raunata Falasdinawa 10, in ji cibiyar yada labarai ta Falasdinu (PIC).
Har ila yau Isra’ila ta tsananta kai hare-hare a duk fadin Gaza, inda aka harba makaman atilari a yankunan kudanci da gabashin unguwar Zeitoun.