Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A ranar Litinin ne jaridar Daily Nigerian ta fitar da wani labari wanda ke zargin cewa gwamnan Kano Abba Kabir ya daina ɗaukar kiran wayar uban gidansa Sanata Rabiu Kwankwaso, lamarin da hakan ya tayar da ƙura a kafofin sada zumunta.
Sai dai a wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamnan Kano kan kafofin sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, ya ce babu wata rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba da mai gidan nasa Kwankwaso.
“Gwamna Abba K Yusuf ya himmatu sosai wajen tabbatar da akidu da hangen nesa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Ya himmatu wajen samar da hadin kai a cikin jam’iyyar tare da yin aiki tare da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar ciki har da Kwankwaso domin cim ma burinmu,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
“Wannan zargin ba gaskiya bane kuma karkatar da hankali ne sakamakon Abba yana da ladabi da alaƙa mai kyau da Rabiu Kwankwaso, inda yake kallonsa a matsayin jagora a jam’iyya da kuma tafiyarsa ta siyasa. Duk wata magana ta ɓaraka a tsakaninsu batu ne kawai na zuzutawa, amma ya saɓa wa mu’amularsu ta aiki,” in ji sanarwar.
A ‘yan kwanakin nan ana ta samun raɗe-raɗin rashin jituwa a tsakanin gwamnan na Kano da kuma Kwankwaso inda har wasu da ba a tabbatar da ko su wane ne ba suka fitar da wata tafiya mai suna Abba Tsaya da Kafarka, wadda ke nufin Abban ya ƙaurace wa Kwankwaso.
A ranar Litinin ne Dan majalisar wakilan jihar daga karamar hukumar Dala Aliyu Sani Madakin Gini da takwaransa na kananan hukumomin Rano da Bunkure da kuma Kibiya a majalisar wakilan kasar suka sanar da barranta kansu da tafiyar Kwankwasiyya a jihar.