Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi hasashen yuwar samun ruwa mai ɗauke da tsawa a faɗin kasar tun daga ranar Litinin, 23 ga Satumba zuwa Laraba 25.
Hasashen wanda NiMet ta fitar a ranar Lahadi ya nuna cewa za a samu ruwan sama da safiyar Litinin a jihohin Sokoto da Kebbi da Borno.
Haka kuma hukumar ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama a Jigawa da Taraba da Adamawa da Gombe da Bauchi da Kano da Katsina da Kaduna da Zamfara da Kebi da Sokoto a ranar Litinin ɗin da rana.
“Akwai yiwuwar samun ruwan sama a wasu sassa na Abuja babban birnin Nijeriya da Neja da Nasarawa da Benue da Filato da Kwara da safe.
“Da rana da dare, ana sa ran samun ruwa a jihohin Kwara da Abuja da Neja da Benue da Kogi.
“Akwai yiwuwar samun ruwan da safe a kudu maso yammaci musamman a sassan Oyo da Ondo da Osun da Ekiti da Ogun har zuwa Legas da Delta da Ribas da Cross River da Akwa Ibom da Bayelsa da safe,” in ji hukumar.
Haka kuma NiMet ɗin ta ce da rana akwai yiwuwar samun ruwan saman a Enugu da Edo da Ebonyi da Ondo da Abia da Osun da Imo da Ekiti da Dekta da Bayelsa da Cross River da Ribas da Legas a ranar Litinin ɗin da rana.
An ta samun ruwan sama mai ƙarfi a ‘yan kwanakin nan a Nijeriyar lamarin da ya jawo ambaliyar ruwa a wasu sassan ƙasar wadda har ta kai ga asarar rayuka.
Ambaliyar dai ta fi ɓarna a ‘yan kwanakin nan a ƙasar ita ce wadda aka samu a birnin Maiduguri na jihar Borno dakr arewa maso gabashin Najeriya, inda aka yi asarar rayuka, gidaje da dukiyoyi mai tarin yawa.