A ranar 11 ga watan Agusta ne, sabon zaɓaɓɓen shugaban na Iran Masoud Pezeshkian ya gabatar da sunayen mutanen da yake so a ba ministoci a gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman ƙuri’ar amincewa.
Dangane da dokar Iran, kakakin majalisar ƙasar zai karanta takardar gabatarwa ta shugaban ƙasar, inda bayan haka sai sauran takardu su biyo baya waɗanda za a miƙa su ga kwamitocin da suka dace domin dubawa.
Waɗannan kwamitocin an kafa su ne domin tantance cancanta da takardu da asali da kuma shawarar bayar da ma’aikatar da ta dace ga kowane minista tare da gabatar da bincikensu ga kakakin majalisa. Haka kuma za a buga takardun wannan rahoto tare da miƙa su ga duka mambobin majalisa domin bitarsu.
Mako ɗaya bayan gabatarwar ta gwamnati, za a yi zama daban-daban a majalisa domin tafka muhawara dangane da tsare-tsare da shirye-shirye na gwamnati tare da gudanar da ƙuri’ar amincewa dangane da ministocin.
A cikin wannan lokacin, ministocin da aka zaɓe su za su aika da shirye-shiryensu ga kwamitocin da suka dace da kuma mayar da martani dangane da duk wata buƙata daga mambobin kwamitin.
Ana saran matakin zai kai ga samun kuri’un amincewa da kowane minista, sannan kuma za a kada kuri’ar amincewa ga daukacin majalisar ministocin kasar.
Majalisar ministocin da Pezeshkian ke son ya kafa
Gabatar da sunayen ministoci da shugaban ya yi ya jawo zazzafar muhawara a kafofin watsa labarai na Iran, inda akasarinsu suke mayar da hankali dangane ko yanayin waɗanda aka zaɓa a ministoci ya zo daidai da alƙawarin da Pezeshkian ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe dangane da irin mutanen da zai yi aiki da su.
Musamman ma, matsakaitan shekarun mambobin majalisar ministocin ya kai kusan shekara 60. Mace daya ce kawai aka zaba, kuma majalisar ministocin kasar mai rinjayen ‘yan Shi’a ba ta da wakilcin ‘yan Sunna.
Idan aka yi la’akari da manyan kalaman da ya rinƙa yi dangane da batun kawo sauyi, da alama majalisar ministocin da ake son kafawa ta yi kama da mai matsakaicin ra’ayi, ta karkata ga ra’ayin mazan jiya maimakon wacce aka yi alkawarin kawo sauyi.