Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Babu Mafaka Ga Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano — Muhyi Magaji
Babban Labari

Babu Mafaka Ga Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano — Muhyi Magaji

August 11, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Muhuyi Magaji Rimingado (1)

Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu (MATFDAT), Alhaji Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa babu wani mutum ko wata hukuma da za a yi wa rangwame a yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi a jihar.

‎Muhyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wani shirin DuniyarMu a Yau, wanda Freedom Radio Kano, inda ya ce duk wanda aka samu yana safarar, sayarwa ko aikata wani laifi da ya shafi miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

‎Ya ce rundunar ta riga ta kai wasu daga cikin waɗanda suka kamu da shan miyagun ƙwayoyi zuwa Cibiyar Gyaran Hali ta Kiru, domin ba su kulawa da kuma taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.

‎Haka kuma, ya bayyana cewa an gurfanar da wasu waɗanda ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi a gaban kotu, yayin da aka rufe wasu shagunan sayar da magunguna saboda karya ƙa’idojin da suka shafi sayarwa, adanawa da sarrafa magunguna.

‎“Babu wanda zai tsira. Duk wanda ke sayarwa ko amfani da miyagun ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu. Babu mafaka ga masu aikata irin wannan laifi a Kano,” in ji shi.

‎Shugaban rundunar ya ce za a ƙara faɗaɗa haɗin gwiwa da malaman addini, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tunkarar matsalar ta hanyar haɗin gwiwa.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa.

August 11, 2026

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.