Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 
Labaran Cikin Gida

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260512 WA02491 (1)

Rikicin da ke girgiza kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ya kamata ya zama lokaci na zurfin tunani ga shugabannin Arewa maimakon ci gaba da fafutukar neman iko. An kafa ACF ne domin hada kan Arewacin Najeriya, kare muradunta, inganta zaman lafiya, da bayar da jagoranci kan al’amuran da suka shafi yankin. Idan rikice rikicen cikin gida suka rikide zuwa zarge zargen cin hanci, killace ofisoshi da ‘yan sanda, da rudanin kundin tsarin mulki, to martabar Arewa gaba daya ce ke tabarbarewa a idanun kasa baki daya.

Abin da ya fara a matsayin sabani tsakanin Kwamitin zartarwa a matakin kasa da Kwamitin Aminttattu, (BoT) yanzu ya bayyana wata babbar matsala ta rashin yarda da kungiyoyin dattawa a tsakanin matasan Arewa. Mutane da dama na zargin irin wadannan kungiyoyi sun zama na manyan ‘yan siyasa, iyalai, da tsofaffin abokan anfani kawai, yayin da ake tuna matasa ne kawai lokacin zabe ko gangamin siyasa, daga baya kuma a yi watsi da su.

Saboda haka, bai kamata rikicin ya kare da dakatarwa ko martanin dakatarwa kawai ba. Ya kamata ya zama wata dama ta yin gyara na gaskiya da sake farfado da kungiyar gaba daya.

Babban darasi da za a iya koya shi ne daga tsarin rundunar tsaro ta Amotekun na yankin Kudu maso Yamma. Duk da cewa manufarsu ta sha bamban, Amotekun ta samu nasara ne saboda hada tsofaffin jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki na al’umma, da sauran jama’a domin cimma manufar kare rayuka da dukiyoyi cikin tasiri. Haka ma Arewa na bukatar sake fasalta ACF daga kungiyar manyan mutane zuwa wata kafa ta jama’a da ke wakiltar muradun manoma, ‘yan kasuwa, dalibai, mata, kwararru, da matasa.

Domin dawo da martaba da kwanciyar hankali, ya zama dole a kafa kwamitin sulhu da garambawul mai zaman kansa, wanda zai kunshi tsofaffin alkalai, dattawa masu kima, sarakunan gargajiya, malamai, kungiyoyin fararen hula, da kwararrun Arewa marasa bangaranci. Wannan kwamiti zai:

Duba kundin tsarin mulkin ACF gaba daya domin ya zama mai wakiltar kowa,

Binciken duk zarge zargen badakala ta kudi,

Samar da hanyoyin tabbatar da gaskiya da rikon amana,

Fayyana iyakokin iko tsakanin bangarorin kungiyar,

Da kuma bayar da shawarwarin da za su bude kofar shiga ga jama’a da dama.

Domin tabbatar da zaman lafiya da sake gina kungiyar, akwai bukatar shugabannin NEC da Kwamitin Aminttattu na yanzu su sauka na wani lokaci domin bai wa tsarin rikon kwarya mai zaman kansa dama. Bayan haka a gudanar da sahihin zabe tare da tuntubar jihohin Arewa baki daya, tare da bai wa matasa muhimmiyar rawa. Tsarin membobinsu ma ya kamata ya zama mai bude kofa ga jama’a maimakon takaita shi ga wasu tsirarun masu fada aji.

Idan kuma bincike ya tabbatar da wawure ko karkatar da kudade, duk wanda aka samu da laifi ko wane matsayi yake da shi , ya kamata ya mayar da kudaden tare da fuskantar hukuncin da ya dace. Rikon amana da gaskiya su ne kadai za su iya dawo wa ACF da martabar da za ta ba ta damar magana da sunan Arewa.

Abu mafi muhimmanci shi ne shugabannin Arewa su fahimci cewa wannan rikici ya wuce rikicin mutane ko mukamai. Babbar matsalar ita ce kara yawaitar gibin da ke tsakanin kungiyoyin shugabanci da talakawan Arewa da ke fama da rashin tsaro, rashin aikin yi, talauci, jahilci, da takaicin rayuwa. Kungiyar da aka kafa domin hada kan Arewa ba za ta iya cigaba da rugujewa saboda rikicin neman iko da anfani kai tsaye ba.

Saboda haka, lokaci ya yi da za a ja layi, a dakatar da rikicin bangaranci, a yi wa kungiyar garambawul cikin jarumta, sannan a gina sabuwar hangen nesa da za ta yi wa talakawan Arewa aiki na gaskiya maimakon kare muradun wasu mutane

Abbas Ibrahim na rubutu daga Kano, kuma ana iya tuntubarsa ta adireshin imel: abbasibrahim664@gmail.com.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026

Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.