Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260401 WA0024(1)

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA, ke fuskantar matsaloli wajen samun magunguna, duk da kasancewarsu cikin tsarin.

Shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA tsari ne na taimakekeniya domin tallafawa masu rauni, musamman mata da tsofaffi, domin samun kulawa ta musamman.

Rahotanni sun nuna cewa, matsalar gudanar da shirin ta fi shafar mata da tsofaffi marasa lafiya.

Wakilanmu sun lura da cewa, matsalar ta fi k’amari a asibitin K’wararru na Asibitin Murtala Muhammad.

Asibitin na daya daga cikin manyan asibitocin da ke karɓar dimbin marasa lafiya daga ciki da wajen jihar.

Malama Hafsat, mai kimanin shekara 41 wadda ke fama da cutar asma, na d‎aya daga cikin wadanda abin ya shafa. Ta koka da cewa duk lokacin da ta je Asibitin domin a duba lafiyarta, takan yi tafiya mai tsawo domin karɓar magunguna daga wani wuri dabam da bangaren da ake duba lafiyarta.

‎A cewarta, sau da dama tana tsallaka titi mai cunkoso tare da kananan yaranta, lamarin da ke jefa ta cikin hadari da kuma kara tsananta mata rashin lafiyarta.

‎“Wani lokaci ma wannan wahalar na iya tayar min da ciwon asma,” in ji ta.

‎Hafsat ta ce daga bisani ta hakura da tsarin, inda ta koma sayen magunguna daga kantuna masu zaman kansu, duk da karin kudin da hakan ke jawo mata.

‎Sai dai bincike ya nuna cewa ba ita kadai ba ce ke fuskantar irin wannan matsala. Wasu masu anfani da shirin, musamman masu karamin karfi, sun daina anfani da shi sakamakon irin wadannan kalubale.

‎Rahotanni sun kuma bayyana cewa, duk da akwai wasu kantunan magunguna a cikin harabar bangaren jinya, ba sa cikin tsarin hukuma, abin da ke kara haifar da tambayoyi kan yadda aka tsara tsarin samar da magunguna.

‎Masu lura da al’amuran lafiya na cewa, wannan gibi na iya zama sakamakon matsalolin gudanarwa ko rashin daidaito tsakanin sassan aiki.

‎Haka kuma, batun ya janyo muhawara kan ko tsarin na cika ka’idojin da suka tanadi samar da ingantaccen kulawar lafiya ga ‘yan kasa.

‎An ruwaito cewa an tuntubi hukumomin da abin ya shafa domin jin karin bayani, amma har yanzu ba a samu amsa a hukumance ba.

‎Yayin da jama’a ke kara dogaro da irin wadannan tsare-tsaren lafiya, ana kira ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalar.

‎Masu sharhi na ganin cewa hada wuraren bada jinya da na karɓar magunguna wuri guda, tare da saukaka hanyoyin karɓar magani ga marasa lafiya, na daga cikin matakan da za su taimaka wajen rage wahalar da ake fuskanta

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.