Rundunar ƴan sanda na jihar Legas ta kama wani mai-gadi, Amos Kini, bisa zargin satar yaro ɗan shekara biyu a unguwar Elemoro.
A sanarwar da kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar a yau Litinin, an ce mahaifiyar yaron ce ta kai rahoto ga ofishin ƴan sanda makon da ya gabata.
Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:50 na dare, lokacin da ma’aikacin tsaronta ya gudu da ɗanta da wayarta ba tare da izini ba.
Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya
Bayan haka, wanda ake zargin ya yi amfani da wayar da ya sace wajen kiran mahaifin yaron, inda ya nemi kuɗin fansa na Naira miliyan biyar (₦5,000,000) kafin ya saki yaron.
Rundunar ta kuma kama wani mutum mai suna Aruna Dauda, wanda ya tsaya wa wanda ake zargi shaida kafin a ɗauke shi aiki, domin gudanar da tambayoyi.
Daga baya, wanda ake zargin ya saki yaron, sai dai rundunar ta ci gaba da bin diddigin shi har sai da aka cafke shi.
“A ranar 23 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, jami’an sashin Tactical Squad (Hyena), bayan samun sahihan bayanai, sun gano inda yake, suka kuma cafke Amos Kini a unguwar Elemoro. Yana hannun ‘yan sanda kuma ya amsa laifinsa. Za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji Adebisi.

