Gwamnatin tarayya tare da guiwa da Gavi da ke samar da magunguna da asusun kula da ƙananan yara (UNICEF), za ta sanya wutar sola a asibitocin a matakin farko (PHCs) guda 371 a jihohi 16 ciki har da babban birnin tarayya Abuja domin inganta allurar rigakafi da kula da marasa lafiya musamman a yankunan da aka bi buƙatar tallafin.
An ƙaddamar da fara shirin saka wutar ne a wani biki da hukumar bunƙasa asibitoci a matakin farko (NPHCDA) ta shirya a Abuja a ranar Alhamis.
Kano, Sokoto da jihohi tara na iya fuskantar ɓarkewar cutar sankarƙau – NiMet
A yayin da yake magana, babban daraktan NPHCDA, Muyi Aina, ya ce, saka wutar solar zai samar da tsayayyiyar wutar lantarki ga asibitocin da ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Mista Aina ya ce tsayayyiyar wutar lantarki na da muhimmancin gaske wajen kula da alurarorin rigakafi da gudanar da ayyukan da za su ceci rayuka kamar allurar rigakafi, da lafiyar mata masu juna biyu da masu neman agajin gaggawa.
Ya ce, wutar lantarki ba abu ne na jin daɗi ba, abu ne da ya zama wajibi wajen gudanar da ayyuka da taimaka wajen hauhuwar yara cikin kwanciyar hankali da daddare.
Inganta asibitoci PHCs:
Mista Aina ya ce, shirin sa wutar solar wani ɓangare ne na ƙarfafa tsarin kiwon lafiya a asibitoci a matakin farko da ba wa mutane damar samun kulawar lafiya.
Ya kuma ce, baya ga wutar salar, gwamnati ta ƙaddamar da shirin farfaɗo da asibitoci a matakin farko a yayin da ake kan gyaran asibitoci 4,000.
Mafi yawan aibitocin da aka yi wa gyara an sa musu wutar sola a yayin da aje ci gaba da sa wutar solar a sauran asibitocin.
Shirin farfaɗo da asibitoci ha haɗa har da samar da kayayyakin more rayuwa kamar wutar lantarki da ruwa da abubuwan tsabtace asibiti tare da magungunan da ake da buƙata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Allurar rigakafin:
Haka kuma, a yayin da take magana, babbar jami’in Gavi, Sania Nishtar, ta ce, kamfanin na su ya zuba hannun jarin sama da Dala biliyan 2.4 a shirin allurar rigakafin Najeriya a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Ms Nishtar, wadda ta wakilci babban manajar Gavi, Edna Harimenshi, ta ce, wannan haɗin guiwa ya ba da gudunmowa wajen inganta yadda aike allurar rigakafi wanda ya karu daga kaso 27% a 2001 zuwa kaso 67% a 2024.
A cewarta, ci gaban ya sa Najeriya ta cike giɓin allurar rigakafi da kai wa ga yaran da ba su samu allurar rigakafi ba.
Ta kuma ce ci gaban ya ta’allaƙa ne da tsayayyiyar wutar lantarki.
“Ƙaddamar da shirin wani mataki ne na magance ƙalubalen da aka daɗe ana fama da su.”
Haka kuma wakilin UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ya yaba wa ƙoƙarin da Najeriya ke yi wajen ƙarfafa asibitoci a matakin farko da faɗaɗa allurar rigakafi.
Ms Abdelatef ta ce wannan shiri a shekarun baya, ya tallafa wa yara waɗanda ba su samu allurar rigakafi ba tare da bayyana da shirin da muhimmin abu da zai rage bambancin da ake samu wajen neman lafiya.
Ta ce tsayyayiyar wutar lantarki a fannin lafiya mihimmin abu ne ga ayyukan allurar rigakafi da lafiyar mata masu juna biyu da sauran ayyukan tallafa wa al’umma.
Ita ma a jawabi, sakatariyar lafiya da muhalli ta birnin tarayya Abuja, Adedolapo Fasawe, ta ce, shirin muhimmi ne wajen inganta asibitoci a matakin farko ga mutane masu rauni,
Ms Fasawe ta ce samar da tsayayyiyar wuta na da muhimmanci wajen kula da allurar rigakafi wadda ke buƙatar wuri mai sauyi da ba da magani da tabbatar da yanayi mai kyau ga mata masu juna biyu a lokacin haihuwa.
Game da shirin Gavi-CDS3:
Shirin Gavi-CDS3, shiri ne da ya ƙunshi masu ruwa da tsaki daban-daban a gida da ƙasashen waje. Cibiyar eHealth Systems Africa ta sa ka wutar lantarki a asibitoci a matakin farko 238 a yayin da kamfanin Differ Community Power ya sa ka wutar lantarki a asibitoci 133 a faɗin Arewa maso gabas.
UNICEF ce ta kula da aikin tare da NPHCDA da hukumar bunƙasa asibitoci a matakin farko da taimakon ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila da.
Jihohin da suka ci gajiyar shirin ciki har da Abuja, sun sha alwashin kula da kayayyakin domin tabbatar da ci gaban ayyukansu.

