Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ba shakka sun tayar da gagarumin rikici na siyasa, kace-nace tare da kara zurfafa rashin jituwa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa na siyasa, Dr Rabiu Musa Kwankwaso.
An tabbatar da cewa akalla ‘yan majalisa 38 ne suka rattaba hannu kan takardar neman tsige mataimakin gwamnan bisa zargin aikata manyan laifuka, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba da kuma karya amana ta jama’a.
Takardar da aka gabatar a zaman majalisar ta ce tana bin tsarin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara), wanda ya fayyace yadda za a tsige mataimakin gwamna daga mukaminsa.
A yayin gabatar da takardar, wani dan majalisa ya bayyana cewa matakin tsige Abdussalam ya samo asali ne daga wasu zarge-zarge da suka shafi aikinsa tun yana Kwamishinan Kananan Hukumomi har zuwa lokacin da ya zama Mataimakin Gwamna.
Takardar ta zargi Abdussalam da karɓar cin hanci daga kananan hukumomi 44 na jihar tsakanin Yuni 2023 zuwa Janairu 2024. ‘Yan majalisar sun ce yana karɓar kusan Naira miliyan 1.5 a kowane wata daga kowace karamar hukuma, wanda ya kai kusan Naira miliyan 66 a wata da jimillar Naira miliyan 462 a cikin watanni bakwai.
Haka kuma, an zarge shi da karɓar karin kudade har Naira miliyan 726 tsakanin Fabrairu zuwa Yuli 2024 a matsayin kudin yin wasu “aikace-aikace na musamman” ga kananan hukumomi.
Majalisar ta kara da cewa Abdussalam ya saba doka ta hanyar taimakawa wajen sakin Naira miliyan 440 daga kananan hukumomi zuwa kamfanin Novomed Pharmaceuticals Limited ba tare da bin dokokin saye da sarrafa kudi na jihar ba.
Majalisar ta ce wadannan zarge-zargen sun kai matsayin manyan laifuka, don haka ta yanke hukuncin cewa a tsige mataimakin gwamnan bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Sai dai Kungiyar Kwankwasiyya Movement, karkashin Dr Rabiu Musa Kwankwaso, ta yi watsi da wannan mataki na majalisar, tana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe kuma kawai neman bata suna ne.
Kungiyar ta gargadi Majalisar Dokokin Kano da Gwamnatin Jihar da su yi taka-tsantsan, tana mai cewa tsige mataimakin gwamnan zai iya kara rarrabuwar kawuna da kuma lalata amanar da jama’a suka ba gwamnati.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, mai magana da yawun Kwankwasiyya, Dr Habibu Saleh, ya bayyana cewa tsige mataimakin gwamnan abin damuwa ne, yana kuma gargadin ‘yan siyasa da su guji daukar matakan da za a iya fassara a matsayin siyasa kawai.
Ya ce: “Mutanen Kano suna kallon abin da ke faruwa, kuma akwai damuwa cewa wannan yunkuri na tsige mataimakin gwamnan siyasa ce kawai ba wai bukatar kundin tsarin mulki ba.”
Saleh ya jaddada cewa tsige mutum babban iko ne da kundin tsarin mulki ya ba majalisa, don haka bai kamata a yi amfani da shi don biyan bukatar siyasa ba.
Ya tunatar da shugabannin jihar cewa nasarar wannan gwamnati ta samo asali ne daga hadin kan dubban magoya bayan Kwankwasiyya a fadin jihar.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa kudin Naira biliyan 1.1 da ake magana akai an amince da shi ne ta hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf, bayan wata wasika da Kungiyar Kananan Hukumomi (ALGON) ta rubuta a watan Afrilu 2024 domin gyaran rijiyoyin burtsatse da samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.
Takardun sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kudin ta ofishin Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam.
Yanzu dai abin jira ne a gani ko Majalisar Dokokin da jam’iyyar APC ke da rinjaye za ta iya tabbatar da cewa an yi almundahana da kudin, in ba haka ba ikirarin Kwankwasiyya na cewa siyasa ce kawai zai iya samun karbuwa.

