Rundunar Kano Neighbourhood Watch Security Corps, wadda gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin tallafawa hukumomin tsaro a matakin al’umma, ta fara samun tasiri duk da cewa ba ta jima da fara aiki ba.
Rundunar ta fara aiki a hukumance a ranar 23 ga Disamba, 2025, kuma a cikin watanni uku da suka gabata, jami’anta sun fara taka rawa a fannoni kamar tattara bayanan sirri, dakile yunƙurin garkuwa da mutane, kai ɗauki lokacin gobara da kuma taimakawa wajen gano masu aikata laifuka.
Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya
Sai dai duk da wannan ci gaba, wasu daga cikin jama’a da masana na ganin cewa har yanzu rundunar na bukatar ƙarin tsari, kulawa da kuma fadada ayyukanta domin cimma burin da aka kafa ta a kai.
Babban Kwamandan Rundunar, Laftanar Kanal Aminu Yusuf Abdulmalik mai ritaya, ya bayyana cewa a matakin farko rundunar ta fi mayar da hankali ne kan gina tsarin aiki, tsarin tura jami’anta domin fara aiki a wasu kananan hukumomi.
A cewarsa, rundunar na cikin wani mataki da ya kira “matakin ƙarfafa tsari”, inda ake ƙara inganta ayyukan rundunar tare da fadada ayyukanta a cikin al’umma.
“Mun fara ganin wasu alamun ƙarfafawa musamman wajen tattara bayanan sirri daga cikin al’umma da kuma saurin amsa kiran gaggawa,” in ji shi.
Shugaban rundunar ya ce jami’an sun fara aiki tare da sauran hukumomin tsaro ta hanyar sintiri da kuma sa ido kan al’amuran tsaro, domin gano matsaloli tun kafin su tsananta.
A cewarsa, sabuwar rundunar ta fara aiki da taimakawa wajen wasu ayyukan tsaro a sassan jihar, Yana mai bayar da misali, na yadda jami’an rundunar suka ba da gudummawa wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka shafi garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga a kananan hukumomin Bagwai, Shanono da Gwarzo.
A Karamar Hukumar Dambatta ma, jami’an rundunar sun taimaka wajen dakile wani yunƙurin garkuwa da wani mutum, sannan suka ba da agaji lokacin da gobara ta tashi a Kasuwar Singa.
Haka kuma a unguwar Dorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale, jami’an rundunar sun taimaka wa hukumomi wajen gudanar da bincike kan wani zargi na kisan kai.
Rundunar Neighbourhood Watch ta Kano na aiki ne bisa wani tsari da aka shimfiɗa domin tabbatar da cewa ayyukan tsaro sun kai ga al’umma, tsarin fa ya haɗa da babbar hedikwatar rundunar a matakin jiha, rundunonin sassa guda biyar, kwamandojin kananan hukumomi da kuma rukunin jami’ai a matakin unguwanni.
Shugaban rundunar ya ce kusantar da jami’an tsaro ga al’umma na daga cikin muhimman ginshiƙan nasarar wannan shiri.
“Yawancin barazanar tsaro na farawa ne daga cikin al’umma. Don haka, idan jami’ai suna kusa da al’umma, lallai hakan zai taimaka wajen gano matsaloli tun da wuri,” in ji Abdulmalik.
Game da yiwuwar amfani da rundunar ta hanyar siyasa ko cin zarafi, shugabannin rundunar sun ce an gudanar da daukar ma’aikata da nade-naden mukamai ne bisa ƙa’idojin ƙwarewa da gaskiya.
Sun ce an yi la’akari da abubuwa kamar haka: ilimi, gaskiya, kwarewar jagoranci da kuma lafiyar jiki da ta kwakwalwa wajen daukar jami’ai.
Rundunar ta kuma kafa dokokin aiki da tsarin ladabtarwa, tare da horar da jami’anta kan haƙƙin bil’adama da kuma yadda za su yi amfani da ƙarfi cikin doka. Haka kuma, Hukumar ba za ta amincewa duk wata manufa ta cin hanci ko cin zarafi ko tsare mutane ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, Jama’a za su iya kai korafe korafensu zuwa ofisoshin kananan hukumomi ko kuma ta January tura sako ta lambobin waya na hedikwatar rundunar da ke harabar KNARDA a kan titin Hadejia.
Duk da irin wannan nasarorin farko da Hukumar ta samu, shugaban rundunar ya amince cewa har yanzu ayyukan hukumar bai kai ga wasu sassan jihar ba.
A cewarsa, hakan na da nasaba da aikin daukar sabbin jami’ai da kuma horo da ake gudanarwa tare da hadin gwiwar Hukumar Ma’aikatan Jiha.
Sai dai ya ce bayan kammala wadannan matakai, ana sa ran jama’a za su fara ganin karin jami’an rundunar a dukkan unguwanni.
A tattaunawa da wani Masani kan manufofin gwamnati, Malam Tijjani Sarki, ya ce rundunar ta na da amfani, kuma za ta iya taimakawa sosai wajen inganta tsaro a matakin al’umma idan aka tafiyar da ita cikin ƙwarewa da adalci.
Sai dai ya jaddada muhimmancin ci gaba da sa ido da kulawa domin kauce wa yiwuwar amfani da iko ta hanyar bai kamata ba.
Ana ta bangaren, Hajiya Khadija Naseer, wata malamar makarantar sakandare, ta ce har yanzu lokaci bai yi ba ta yadda za a iya tantance tasirin rundunar gaba ɗaya, kasancewar sabuwa ce har yanzu.
Shi kuwa wani dan kasuwa a Kasuwar Kwari, Yasir Sani Abdullahi ya buƙaci a ƙara yawan jami’an Kano Neighbourhood Watch Corps domin ƙarfafa tsaro a faɗin Jihar Kano.
Ya ce duk da cewa ɗaukar jami’ai 2,000 da gwamnatin jihar ta yi wani mataki ne mai kyau, amma adadin na iya zama bai wadatar ba idan aka yi la’akari da yawan al’ummar da ke rayuwa a cikin jihar da kuma faɗin yankunan da suke buƙatar kulawar tsaro.
Abdullahi ya bayyana cewa domin tabbatar da ingantaccen tsaro a matakin al’umma, ya kamata a ƙara yawan jami’an zuwa akalla 10,000, domin su samu damar isa yankuna da dama na birane da karkara.
Ya ƙara da cewa tsaro na da matuƙar muhimmanci ga zaman lafiya da ci gaban al’ummar Jihar Kano, yana mai jaddada cewa ƙarfafa irin wannan tsarin tsaro na cikin gida zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugabannin rundunar sun ce a halin yanzu abubuwan da suka fi mayar da hankali a kai sun haɗa da kammala tura jami’ai a dukkan unguwanni, ƙarfafa ladabi da bin doka, da kuma ƙara haɗin gwiwa da al’umma, yayin da al’umma ke fatan an gudanar da Hukumar ta hanyar da ya kamata, ba tare da amfani da ita ba wajen muzgunawa al’umma ba.

