Ƴanta’adda sun kashe mayakan sa-kai akalla 25 yayin wani harin da suka kai ƙauyuka hudu na jihar Tillabery da ke yammacin jamhuriya Nijar.
Majiyoyi sun sun ce ƴanta’addan sun kai harin ne ranar 26 ga watan Fabarairu 2026 a yankin Anzourou da ke kan iyaka kasar da Mali.
Iran Ta Tabbatar Da Kisan Ali Khamenei Da Iyalansa
Dakarun sa-kan na aikin tabbatar da tsaro a kauyukansu ne lokacin da ƴanta’addan suka far musu.
Wanan harin na zuwa a daidai lokacin da mayaka masu ikirarin jihadi ke cigaba da kwarara a yankin da matsalar tsaro ta yiwa illa.
A makwonni uku da suka gabata ma ƴanta’adda sun kaiwa wani sansanin dakarun Nijar da ke garin Ayorou na jihar Tillabery hari.
Gabanin haka ƙungiyar IS mai da’awar kafa daular muslunci ta dauki alhakin kai harin filin tashi da saukar jiragen Yamai wanda ya haifar da gagarumar barna ga sansanin sojin saman kasar mai lamba 101.

