Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, a matsayin Shugaban Kwamitin Ciyarwar Azumin Ramadan na Ƙasa.
Wannan shiri na gwamnatin tarayya zai kula da rabon kayan abinci kamar shinkafa, gero da mai ga al’umma a duk faɗin Najeriya, domin rage raɗaɗin rayuwa a wannan wata mai alfarma.
Da Dumi Dumi An ga watan Azumi a Nijeriya
Sarkin ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa shiri ne mai muhimmanci, tare da alƙawarin bada cikakken goyon baya domin nasarar sa.

