Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Najeriya: Fiye da rabin mata masu juna biyu na fama da ƙarancin jini, in ji Gwamnatin Tarayya 
Labaran Cikin Gida

Najeriya: Fiye da rabin mata masu juna biyu na fama da ƙarancin jini, in ji Gwamnatin Tarayya 

January 29, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
images (6)

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kusan kashi 58 cikin 100 na mata masu juna biyu a Najeriya na fama da matsalar ƙarancin jini, sakamakon rashin cin abinci mai wadataccen sinadaran gina jiki.

Shugabar sashen kimiyyar gina jiki a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Helen Achimugu, ce ta bayyana hakan ranar Talata a Abuja, yayin wani taron horas da manema labarai da ƙungiyar Civil Society–Scaling Up Nutrition in Nigeria (CS-SUNN) ta shirya.

Taron, wanda ya mayar da hankali kan rawar da manema labarai za su taka wajen yaƙi da matsalar ƙarancin jini a jiki, ya tattauna illolin da matsalar ke haifarwa ga mata masu juna biyu da yara ƙanana, da kuma hanyoyin da za a bi wajen rage ta.

Achimugu ta ce sakamakon binciken lafiya da yawan jama’a na ƙasa (NDHS) na 2023 ya nuna cewa kusan rabin adadin mata masu haihuwa na fama da ƙarancin jini, lamarin da ke jefa lafiyar mata da jarirai cikin hatsari.

Ta bayyana cewa matsalar na da mummunar illa ga yara, inda ta ce Najeriya ce ƙasa ta farko a Afirka, kuma ta biyu a duniya, wajen yawan yaran da ba sa samun girma yadda ya kamata.

“A Najeriya, akwai yara miliyan 35 da ke fama da rashin girman jiki, miliyan 14 na fama da rama, yayin da miliyan 24 ke fama da ƙarancin jini,” in ji ta.

Ta jaddada cewa matsalar ba ta shafi lafiyar al’umma kaɗai ba, har ma tana hana ci gaban tattalin arziki da na ilimi.

Achimugu ta ce matsalar da ake kira “boyayyar yunwa”—wato rashin samun muhimman sinadaran gina jiki—na yaduwa sosai tsakanin yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu, musamman a yankin Arewacin Najeriya.

“Ana kiran ta boyayyar yunwa ne saboda alamunta ba sa bayyana kai tsaye, sai dai a rika ganin sauye-sauye kamar raguwar kaifin basira, gajiya da raunana jiki,” ta ƙara da cewa.

Ta bayyana cewa rashin samun sinadaran gina jiki kamar iron, iodine, zinc, folate da vitamin A na haddasa matsaloli kamar rama, rashin girma yadda ya kamata da nakasar kwakwalwa.

A cewarta, a ƙasashe masu tasowa, rashin wadataccen abinci mai inganta garkuwar jiki na da alaƙa da kusan kashi 60% na cututtuka kamar gudawa, amai, zazzabin cizon sauro da cutar tarin fuka.

Ta ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai da dama domin shawo kan matsalar, ciki har da wayar da kan al’umma kan abinci mai gina jiki, inganta lafiyar mata da yara, da kuma rarraba maganin Multiple Micronutrient Supplements (MMS) ga mata masu juna biyu.

Achimugu ta ce kwalba ɗaya ta MMS na wadatar mace tsawon watanni shida, kuma na taimakawa wajen rage haɗarin zubar jini yayin ciki da haihuwa.

Taron ya horar da manema labarai 39 daga jihohin Nasarawa, Kano, Kaduna, Lagos, Niger, Bauchi da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A nasa jawabin, Shugaban CS-SUNN, Sunday Okoronkwo, ya buƙaci manema labarai da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen wayar da kan jama’a kan illolin ƙarancin jini a jiki, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen samun nasara a yaƙin da ake yi da matsalar, musamman tsakanin mata da yara ƙanana.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026

Maki shida ne ya rage tsakanin Arsenal da Man City

April 13, 2026

Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa

April 13, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.