Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da rahotanni da ke alaƙanta cewa yana daf da komawa wata jam’iyya, da kuma batun cewa zai shiga haɗaka da wasu jam’iyyu, lamarin da ya ce ƙanzon kurege ne kawai domin ba da yawunsa ba.
Dan takarar shugaban ƙasa karashin jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, ya ce raɗe-raɗen ba su da tushi balle makama kuma labaran ƙarya ne kawai na siyasa.
“Na daina yin tsokaci kan lamuran siyasa da ke faruwa a Najeriya… kuma zan ci gaba da yin haka har zuwa wani lokaci,” in ji Rabiu Kwankwaso.
Don haka ne, ya buƙaci al’umma da su amince da sakonni da suka fito daga shafukansa da kuma majiyoyi da aka yarda da su kaɗai ba daga wasu wurare na daban ba.