Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎
Afrika

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Health

A makon da ya gabata, wasu jihohi biyu da babban birnin tarayya, Abuja, sun fuskanci barkewar cututtuka daban-daban, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma da hukumomin lafiya a Nijeriya.
‎
‎‎Adamawa: Cutar Kuraje Ta Buruli Ulcer Ta Kashe Mutum Bakwai
‎‎Jihar Adamawa ta samu barkewar cuta mai zagwanye naman jiki, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cutar a matsayin Buruli Ulcer, wadda ake samun ta a karkara musamman wuraren da ke kusa da ruwa.
‎
‎Dr. Adesigbin Olufemi na shirin kasa na dakile cutar tarin fuka da kuturta a Nijeriya ya bayyana cewa, an samu mutane 67 da ke dauke da cutar, yayin da za a yi wa mutum 8 tiyata. “Ba a gano dalilin barkewar cutar ba, amma bincike na ci gaba,” in ji shi.
‎‎
‎Abuja: Zazzabi Mai Aman Jini Ya Jefa Jama’a Cikin Fargaba
‎‎Babban birnin tarayya, Abuja, ya fuskanci barkewar wata cuta da ke haddasa zazzabi da aman jini. An samu mutum biyu a asibiti tare da alamun cutar da suka hada da zubar jini daga baki, hanci da dubura.
‎‎Bayanan farko sun nuna cewa daya daga cikin mutanen ya yi tafiya zuwa Rwanda kafin ya fara fuskantar alamun cutar. Hukumomin NCDC sun fara gwaje-gwaje don gano ko cutar na da alaka da Ebola, Marburg, Dengue ko Lassa.
‎‎Hukumomi sun yi gargadi ga jama’a da su kula da shigi da ficin mutane, musamman a wuraren kasuwanci da taron jama’a.
‎
‎‎Kaduna: Barkewar Mashako Ta Tilasta Rufe Makarantu
‎‎A jahar Kaduna, cutar Mashako ta kashe yara biyu a Karamar Hukumar Birnin Gwari, inda aka rufe makarantun jihar na tsawon mako guda.
‎‎Kwamishiniyar lafiya, Dr. Umma Kulthum Ahmed, ta ce rufe makarantu mataki ne na hana yaduwar cutar a tsakanin dalibai. Fiye da mutane 40 aka killace, wasu kuma daga cikinsu aka sallama daga asibiti.
‎
‎‎Hukumomi sun yi kira ga al’umma da su kara tsaftar muhalli, bin ka’idojin lafiya, da kuma sanar da asibitoci duk wani mutum da ya fara fuskantar alamun cuta. Barkewar wadannan cututtuka uku ya nuna cewa akwai bukatar a dage wajen wayar da kan jama’a da kuma hanzarta dakile yaduwar cutuka.
‎

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

October 20, 2025

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

October 20, 2025

Kano: KIRS Ta Fitar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Ta Hanyar Fasahar Zamani

October 6, 2025

Kwalara ta kashe mutane 4,778 a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024

October 6, 2025

NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya

October 6, 2025

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi malamai kan binciken kwamitin Shura

October 6, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsohon Gwamna Na Fuskantar Bincike Kan Zargin Hannu a Shirin Juyin Mulki

By WafsymOctober 20, 2025

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna daga wani yanki na kudu na ƙasar nan wanda…

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya

September 27, 2025

Barkewar Cututtuka Uku Sun Tayar da Hankalin Hukumomin Lafiya a Nijeriya ‎

September 27, 2025

DALILAN DA YASA MUKAYI GWANJON TSAFFIN MOTOCIN DA MUKE GUDANAR DA AIKIN MU- NDLEA

April 13, 2025
© 2025 WDN HAUSA
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.