Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta kama wasu manyan masu safarar ƙwayoyi dake da hannu a shirin fitar da ɗaurin ƙwaya guda 6 daga ƙasar zuwa Ingila.
Hukumar ta samu wannan nasara ne bayan aikin da ta shafe makonni 3 tana gudanarwa a jihar Lagos, wanda ya kai ga kame mutane 6, ciki har da shugabansu Alhaji Hammed Ode.
Jami’in Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a Lahadin nan.
Babafemi ya ce sun fara gudanar da aikin ne tun ranar 16 ga watan Satumbar 2025, inda jami’ansu na filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos, suka kame ɗaurin ƙwayoyi 174 mai nauyin kilogiram 13.4.
Ƙwayoyin an boye sune cikin robobin man shafawa da nufin safararsu zuwa waje.
A ‘yan shekarun nan, hukumar NDLEA ta sha yin kamen tarin ƙwayoyi da ake ƙoƙarin fitar dasu daga ƙasar ta Afrika zuwa Birtaniya da sauran ƙasashen duniya
