Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kano (KIRS) ta kaddamar da wani sabon tsari na zamani da nufin sauya yadda al’umma ke biyan haraji a fadin jihar, tare da tabbatar da inganci, gaskiya da sauƙi a tsarin tattara kudade.
Sabon tsarin, wanda ya fito ne a ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na ƙara yawan kudaden shiga na cikin gida da rage dogaro da tallafin gwamnatin tarayya, ya mai da hankali kan amfani da fasahar zamani da haɗa bayanan masu biyan haraji da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN). Wannan, a cewar hukumar, zai taimaka wajen gano masu kauce wa biyan haraji da kuma hana maimaita rajista da sunaye daban-daban.
Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi malamai kan binciken kwamitin Shura
A karkashin tsarin, duk wanda yake da hakkin biyan haraji a jihar dole ne ya yi rajista da KIRS ta amfani da NIN dinsa. Haka kuma, an tanadi sabbin hanyoyi masu sauƙi na biyan haraji ta yanar gizo, ta na’urorin POS, ko kuma kai tsaye ta bankuna.
Babban Daraktan Sashen Tabbatar da Biyan Haraji da Tilastawa na hukumar, Muhammad Abba Aliyu, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da KIRS ta shirya tare da haɗin gwiwar Kungiyar Tabbatar da Kyakkyawan Shugabanci (PACC).
Ya ce: “Wannan sabon tsari zai sauƙaƙa hanyoyin biyan haraji ga al’umma tare da tabbatar da tsafta da gaskiya a tsarin. Duk kudaden da aka tara za su shiga asusun gwamnatin jihar Kano kai tsaye, ba tare da sun ratsa hannun wasu jami’ai ko wasu asusu na daban ba.”
Aliyu ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba da haɗin kai wajen biyan haraji domin bai wa gwamnati damar samun kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar jama’a
