Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce cikin waɗanda aka kama har da wani mutum da ya yi ƙoƙarin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.
Jami’in Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano
Wannan samame ya biyo bayan bayanan sirri ne da hukumar ta samu, kuma an gudanar da shi ƙarƙashin jagorancin Babbar Daraktar NAPTIP, Binta Adamu Bello.
Adekoye ya ce cikin waɗanda aka kama akwai wani babban jami’in tsaro da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu safarar mutane a yankin kudu maso yamma na ƙasar.
> “Mun kuɓutar da yara da matasa masu shekaru tsakanin 15 da 26, waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi, Sudan, Masar, Saudiyya, Bahrain da Afghanistan,” in ji shi.
Adekoye ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kuɓutar ta bayyana cewa za ta tabbatar da an gurfanar da mahaifinta a kotu kan yunƙurin safararta da ya yi zuwa Iraƙi.
Haka kuma, wata daga cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahaifiyarta ce ta tilasta mata ta amince da tafiya zuwa Turai domin yin aiki da za ta rika samun daloli.
Hukumar NAPTIP ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai sama-samar da ayyuka na musamman tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da safarar mutane da kuma tabbatar da cewa duk wanda aka kama da hannu a irin wannan laifi ya fuskanci hukunci.
