‎Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro.

‎Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro.
‎‎Rahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ’yan sanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru.

Jami’an Ƴan sanda Sun Kama Mai-Gadi Da Ake Zargi da Sace Yaro Ɗan Shekara Biyu ‎
‎Wata majiya ta ce, yayin da bindigarsa ƙirar AK-47 ke rataye a wuyansa, sai ya matsa kunamar bindigar bisa kuskure.

‎“An samu bindigar, mai lambar rajista GT 4177, tare da harsashi ɗaya da aka harba. An lissafa harsashi 29 daga cikin 30 da aka ba shi,” in ji majiyar.

‎An garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
‎‎An ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin domin yin bincike.

‎Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa har yanzu ana bincike kan lamarin, kuma za su bayyana sakamakon nan gaba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version