‎Rundunar ƴan sanda na jihar Legas ta kama wani mai-gadi, Amos Kini, bisa zargin satar yaro ɗan shekara biyu a unguwar Elemoro.

‎A sanarwar da kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar a yau Litinin, an ce mahaifiyar yaron ce ta kai rahoto ga ofishin ƴan sanda makon da ya gabata.

‎Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:50 na dare, lokacin da ma’aikacin tsaronta ya gudu da ɗanta da wayarta ba tare da izini ba.

Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya
‎Bayan haka, wanda ake zargin ya yi amfani da wayar da ya sace wajen kiran mahaifin yaron, inda ya nemi kuɗin fansa na Naira miliyan biyar (₦5,000,000) kafin ya saki yaron.

‎Rundunar ta kuma kama wani mutum mai suna Aruna Dauda, wanda ya tsaya wa wanda ake zargi shaida kafin a ɗauke shi aiki, domin gudanar da tambayoyi.

‎Daga baya, wanda ake zargin ya saki yaron, sai dai rundunar ta ci gaba da bin diddigin shi har sai da aka cafke shi.

‎“A ranar 23 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, jami’an sashin Tactical Squad (Hyena), bayan samun sahihan bayanai, sun gano inda yake, suka kuma cafke Amos Kini a unguwar Elemoro. Yana hannun ‘yan sanda kuma ya amsa laifinsa. Za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji Adebisi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version