Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sanar da soke duk wasu buƙatun neman biza da aka shigar.

Ta buƙaci masu neman shiga ƙasarta su duba saƙonninsu na imel don samun cikakkun bayanai kan mataki na gaba.

Shugaban INEC ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ofishin Jakadancin Amurkar ya ce za a ci gaba da gudanar da tantance neman bizar a ofishin jakadancinta da ke Legas.

Sanarwar ta ce jami’anta za su ci gaba da duba bayanan ƴan Amurka ne kawai a yanzu musamman ga masu buƙatar gaggawa.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta buƙaci jami’anta da ke aiki a Najeriya su yi gaggawar barin ƙasar, saboda dalilai na tsaro.

Amurkar ta ce duk waɗanda ayyukansu ba su zama wajibi ba, da ke a ofishin jakadancinta a birnin tarayya Abuja, su tattara kayansu da iyalai domin barin ƙasar.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Amurkar ta kuma lissafa wasu jihohin Najeriyar 23 daga kudu da arewacin ƙasar, inda ta ce suna da haɗari, kuma ta gargaɗi ƴan ƙasarta su guji tafiya zuwa waɗannan jihohin da ta ɗora su a mataki na huɗu na gargaɗi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version