Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya sanar da rushe Majalisar Zartarwa ta jihar, a wani mataki da ke nuna sauyi a harkokin siyasar jihar.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin taron Majalisar Zartarwa karo na 53 da aka gudanar a fadar gwamnati.
Ko da yake bai fayyace dalilan ɗaukar wannan mataki ba, alamu na nuna cewa rushewar na da nasaba da yadda wasu daga cikin kwamishinoni ke nuna sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa
Rahotanni sun ce matakin na da nufin bai wa irin waɗannan mambobi damar bin muradunsu na siyasa ba tare da tangarɗa ba, tare da kauce wa duk wani rikici.
Shugaban INEC ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai
Haka kuma, ana kallon wannan ci gaba a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen siyasa da ake hasashen faruwarsu gabanin zaɓuka masu zuwa a jihar.
Ana sa ran Gwamna Inuwa Yahaya zai sanar da sabuwar majalisar zartarwa nan gaba kaɗan, domin ci gaba da tafiyar da harkokin mulki cikin ƙwarewa da inganci.
