Hukumar kula da gyaran hali ta najeriya (NCOS) reshen jihar Kano ta kama ‘yan mata biyu bisa zargin ƙoƙarin shigar da abin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne cikin gidan gyaran hali da ke goron dutse.
An kama su ne a ranar 21 ga Disamba, 2025, yayin binciken tsaro na yau da kullum a wajen shiga gidan yarin, inda jami’an tsaro suka cafke su suna ƙoƙarin samun izinin shiga. Wadanda aka kama su ne Maryam Ali da Hauwa Musa, mata ‘yan shekaru tsakanin 19 zuwa 20, mazaunan Kano, kuma an same su da wasu abubuwan da ake zargin ƙwayoyi ne da ake shirin kai wa wasu fursunoni.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara
Sanarwar da mai magana da yawun hukumar a jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar ta bayyana cewa an mika waɗanda ake zargin ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin shari’a. Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na tsauraran matakan tsaro, bin ƙa’ida, da rashin sassauci ga duk wata aikata laifi a cikin ko wajen gidan gyaran hali, tare da gargadin jama’a su riƙa bin dokokin ziyartar fursunoni.
