Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga Disamba, 2025, tare da 1 ga Janairu, 2026, a matsayin hutu domin bikin Kirsimeti, Ranar Boxing Day, da kuma sabuwar shekara.
Sanarwar ta fito ne cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Ciki, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a madadin Ministan Harkokin Ciki, Olubunmi Tunji-Ojo, a ranar Litinin.
Nazari: Haɗin Kai, Masana’antu da Ra’ayin Jama’a Kan Makomar Kano
Ministan ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen tunani kan ƙauna, zaman lafiya da sadaukarwa, tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, ingantaccen tsaro da ci gaban ƙasa, yana kuma yi wa al’umma fatan barka da Kirsimeti da sabuwar shekara mai albarka.
