Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta fara aiwatar da cikakken haramcin ɗaukar fasinja a kan babura, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu kananan hukumomi.

Dokar, wacce gwamnatin jihar ta kafa a baya, tana shafar Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yanki na Jido) da Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido Ward).

‎Kano: Duk Wanda Aka Kama Yana Achaba Za A Kwace Masa Babur Tare Dadaurin Watanni 6 Da Tara ‎ ‎— Kwamishinan Shari’a

Kwamishinan ‘Yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi masu babura da adaidaita sahu da su bi dokokin, inda ya ce duk wanda aka kama yana karya doka zai fuskanci hukunci.

Haka kuma, rundunar ta bukaci jama’a su kai rahotan duk wani aiki na rashin tsaro ta hanyar layukan gaggawa na ‘yan sanda.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴansandan, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta bayyana cewa jami’an ‘yansanda da na KAROTA zasu tabbatar da abin dokar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version