Gwamnatin Jihar Kano ta sake tunatar da jama’a cewa duk mai aikin ɗaukar fasinja da babur (Achaba) a wasu yankuna na birnin zai fuskanci hukuncin daurin watanni 6, tara N10,000 ko duk biyun, tare da kwace babur, idan aka kama yana karya doka.

‎Abdulkarim Kabiru Maude, SAN Babban Lauya Gwamnati, Kuma Kwamishinan Sharia Na Jihar Kano ne ya bayyana hakan  ga manema labarai

Datti Baba-Ahmed ya ce ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro “bai da amfani”

‎”Ya  ce dokar hana Achaba ta shafi Kananan Hukumomin: Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo, Dawakin Kudu, Fagge, da Kumbotso.”

‎Ga sauran Kananan Hukumomin da aka amince da Achaba, gwamnati ta ce masu sana’ar dole su yi rajista da Mai Unguwa, Sashen Ayyuka na Karamar Hukuma da Ofishin ‘Yan Sanda domin inganta tsaro a harkar sufuri.

‎Kwamishinan Shari’a, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tsaurara matakai domin tabbatar da tsaro da doka, tare da kira ga shugabannin al’umma da masu sana’ar Achaba da su yi biyayya ga doka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version