Aƙalla, mutane 4,778 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar kwalara a Najeriya, tsakanin shekarar 2020 and 2024, a cewar hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a ƙasar(NCDC).

Alƙaluman hukumar sun nuna cewa a shekarar 2020, mutum 3,513 ka yi zaton sun kamu da cutar, kuma a cikinsu mutum 95 sun mutu.

Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi kan kudi N70,000 ta sanya a zukatan yan Nijeriya

Sai dai alƙaluman sun ƙaru matuƙa a shekarar 2021, inda aka yi zaton mutane 111,062 suka kamu da cutar, kuma 3,604 suka mutu a jihohi 33 na ƙasar.

A shekarar 2025 kaɗai fiye da mutane 300 ne suka mutu, ciki har da mutuwar mutane 179 da sanarwar gwamnatin jihar Zamfara ta ce sun mutu a jihar cikin mutum 12,052 da ake zaton sun kamu da cutar a watan Satumba na 2025.

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau ya tabbatar da mutuwar mutum 58 cikin mutane 258 da ake zaton sabbin kamuwa ne da cutar ta kwalara a ƙananan hukumomi 14 na jihar.

Mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne makonni biyu da suka gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Hakan na faruwa ne duk da miliyoyin dalolin da ƙasar ta samu bashi daga babban bankin duniya don samar da ruwa, muhalli mai tsafta da kuma wasu tallafin dalar Amurka miliyan biyu da ƙasar ta samu daga Majalisar Ɗinkin Duniya don samar da rigakafin kwalara.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version