Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da korar dukkan kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke cikin gwamnatinsa.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun gwamnan, Nelson Chukwudi, ya fitar a daren Laraba daga Fatakwal, ta ce korar ta fara aiki nan take, bayan hukuncin Kotun Koli da aka yanke kwanan nan.
Yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya
A yayin zaman bankwana da ya yi da mambobin majalisar zartarwarsa domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai, Gwamna Fubara ya gode wa dukkan jami’an da suka yi aiki tare da shi a cikin shekaru biyu da suka gabata bisa gudummawar da suka bayar ga ci gaban jihar, kamar yadda Punch ta rawaito.
A cikin jawabin nasa, Gwamnan ya jaddada muhimmancin bikin ƴancin kai, inda ya yi kira ga ƴan Najeriya da su haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu domin gina ƙasa mai cike da zaman lafiya, tsaro da wadata ga kowa da kowa.
Ya kuma tabbatar da aniyar sa na ci gaba da yi wa jihar Rivers hidima da sabon karfi da kuzari, tare da gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke ba shi.
Tun da farko, tsohon shugaban rikon gwamnati na jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (ritaya), wanda aka naɗa lokacin da aka kafa dokar ta-baci a jihar, shi ma ya dakatar da kwamishinoni, masu ba da shawara da shugabannin hukumomi da Fubara ya naɗa.
Sai dai tun bayan tafiyar Ibas daga jihar ranar 18 ga Satumba, ba a san makomar waɗannan jami’an gwamnati ba, lamarin da ya sa majalisar dokokin jihar ta bukaci Gwamna Fubara da ya gabatar da sabbin sunayen kwamishinoni domin tantancewa, tare da kasafin kudin 2025
