Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na gyara da kare gandun daji, yayin da ta kaddamar da sabbin ma’aikata 100 da za su kula da gandun daji 45 a fadin jihar.
Hakan na kun shine ta cikin wata sanarwar da Maryam Abdulqadir Shugabar Sashimi Wayar Da Kai ta Ma’aikatar Muhalli da Kula da Sauyin Yanayi ta jihar ta fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya ce an dauki ma’aikatan ne daga kauyukan da ke kusa da gandun dajin domin sauƙaƙa musu aiki da bayar da rahoto cikin sauri.
Kwamishinan ya yi gargadi ga sabbin jami’an da su rika lura da duk wani barna a cikin gandun daji, ciki har da sare bishiya ba bisa ka’ida ba, mamaye kasa, da amfani da chainsaw ba tare da lasisi ba.
