Attajirin ɗan kasuwar Najeriya kuma hamshaƙin mai kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, na duba yiwuwar gina sabuwar matatar mai mai ƙarfin tace ganga dubu 650 a kullum a ƙasar Kenya kamar yadda TRT Afrika ta rawaito.

Rahotanni sun ce Dangote ya fi karkata wajen gina matatar a birnin Mombasa saboda tashar jirgin ruwanta mai girma da zurfi. Ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin Kenya ya fi girma a yankin Gabashin Afirka, tare da yawan masu amfani da albarkatun mai.

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

Dangote ya ce komai yanzu yana hannun shugaban Kenya, William Ruto, wanda zai yanke hukunci kan aikin.

An kiyasta cewa aikin gina matatar zai lashe tsakanin dala biliyan 15 zuwa 17.

A watan da ya gabata ne shugaban Kenya ya bayyana cewa ƙasashen Gabashin Afirka na tattaunawa kan gina haɗaɗɗiyar matatar mai a Tanzaniya, wadda za ta yi koyi da matatar Dangote da ke Legas.

Matatar Dangote ta dala biliyan 20 da ke Lagos ta fara aiki ne a shekarar 2024.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version