Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soki yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur a ƙasar.
Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron shekara-shekara na The Niche Annual Lecture 2026 da aka gudanar a Legas, inda ya ce bai dace a dena bada tallafin mai ba amma a ci gaba da karɓar bashi ba tare da ganin amfanin hakan ba.
An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje
Ya ce cire tallafin ya zama dole saboda tsadar da yake haifarwa, tare da nuna cewa yanzu Najeriya ta fara tace mai a cikin gida maimakon shigo da shi daga waje, lamarin da ya kamata ya inganta tattalin arziki.
Sai dai ya jaddada cewa ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan daidaita harkokin kuɗi, yana mai tambayar dalilin da ya sa ake ci gaba da karɓar bashi duk da cewa an samu kuɗaɗen da ake kashewa a baya kan tallafi.
Kazalika, Sunusi ya kuma kare wasu muhimman sauye-sauye kamar cire tallafi da sassauta tsarin canjin kuɗi, amma ya nuna damuwa kan yadda aka aiwatar da su, yana cewa rashin tsaurara tsarin kula da yawan kuɗin da ke yawo ya janyo faɗuwar darajar naira.
Ya ƙara da cewa cire tallafin ya zama tilas ne a lokacin da kusan dukkan kuɗaɗen shiga na gwamnati ke tafiya wajen biyan bashin ƙasa, amma ya gargaɗi cewa dole ne a aiwatar da manufofi cikin tsari domin kauce wa ƙarin matsin tattalin arziki.
