Hon.Sha’aban ya jaddada janye neman takarar Sanatan Kaduna ta Arewa, tare da bayyana goyon duk wanda APC ta tsayar
Cikin wata sanarwa da Iyalan Hon. Sani Sha’aban, Danburan Zazzau kuma Barden Keffi, suka fitar dauke da sanya hannun Alhaji Ahmad Bamalli ta bayyana cewar bisa wasu dalilai bayan shawarwarin da aka tattauna daga wannan rana ta Talata 21/4/2026 muna sanar da dukkannin magoya bayan Hon. Sani Sha’aban cewar ya janye daga neman takarar kujerar Sanata a Shiyyar Kaduna ta Arewa wato (zone one), tare da bayyana goyon baya ga duk dan takarar da APC ta tsayar.
A cikin sanarwar an bayyana cewa an dauki wannan mataki ne na janye tamarar ne daga ne bisa la’akari da muradun iyalansa.
Sanarwar ta ce: “Hon. Sha’aban yana nan daram kan wannan matsaya, kuma ba zai nemi wata kujera ta siyasa a jihar ba. Har ila yau, zai cigaba da biyayya ga jam’iyyar APC, kuma a shirye yake ya bayar da gagarumar gudunmawa domin samun nasarar APC a Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa Hon. Sha’aban ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga duk wanda jam’iyyar ta tsayar a matsayin dan takara a kowacce kujera a Jihar Kaduna dama kasa baki daya.
Haka kuma, sanarwar ta yi kira ga dukkan magoya bayan Sha’aban, mambobin jam’iyya, da al’ummar Kaduna ta Arewa da su mutunta tare da fahimtar wannan mataki, yana mai nuna yadda da duk“abin da Allah Ya kaddara.”
Sanarwar ta nuna godiya ga daukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa ci gaba da fatan alheri, addu’o’i, da goyon baya ga Hon. Sani M. Sha’aban.
Ahmad Bamalli ya sanya hannu kan sanarwar a madadin daukacin iyalan Hon. Sani Sha’aban.

