Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya buƙaci dakarun tsaron ƙasar su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƴanbindiga a jihohin arewa maso yamma, inda ya nanata cewa dole a tabbatar Najeriya da ƴan Najeriya sun samu tsaro “ta kowane hali.”
Janar Oluyede ya bayyana haka a ziyarar da ya kai wa sojojin da suke aiki na musamman na Fansan Yamma a garin Gusau da ke jihar Zamfara.
Kotu ta bayar da sammacin kama tsohuwar ministan Buhari Sadiya Faruk bisa zargin badakalar kudade
“Saƙona a fayyace yake: dole dakaru su fita su bi ɓatagari har maɓoyarsu su kawo ƙarshensu. Dole mu tabbatar da tsaron Najeriya ta ko wane hali.”
Hafsan ya bayyana shirin rundunar tsaron Najeriya na kawo ƙarshen matsalolin ƴanbindiga a jihohin arewa ta yamma, inda ya ƙara da cewa idan aka cigaba da matsa wa ƴanbindigar lamba ne za a samu sauƙi da zaman lafiyar da ake buƙata.
Janar ɗin ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Zamfara da ƴan jihar bisa irin gudunmuwar da suke ba jami’an tsaro.
