Babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin mai shari’a Jude Onwuegbuzie ta bayar da sammacin kama tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, da babban sakatare na ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, bisa zargin karkatar da kudade.
Hukumar EFCC na tuhumar su da laifuffuka 21 da suka hada da cin amanar aiki da karkatar da kimanin dala miliyan 1.3 da kuma sama da naira miliyan 746.
‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu
Ana sa ran a gurfanar da su a kotu, amma ba su halarta ba, inda mutum na uku kawai, Sani Nafiu Mohammed, ya bayyana. Lauyan gwamnati ya ce an dade ana kokarin gabatar da su tun Disambar 2025, amma ba a same su ba, duk da cewa an bada su beli.
Lauyan Sadiya ya danganta rashin zuwanta da rashin lafiya, amma kotu ta ki amincewa da hujjar da aka gabatar. Daga nan kotu ta amince da bukatar EFCC na bayar da sammacin kama su.
An dage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga Mayu, 2026 domin fara shari’a.
