Tsagin jam’iyyar ADC da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ke jagoranta, ya kori Nafiu Bala, wanda ake kallonsa a matsayin shugaban wani bangare na jam’iyyar, bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam’iyya.
Haka kuma jam’iyyar ta kori wasu jiga-jigai da suka hada da ɗan majalisar wakilai Leke Abejide, da Kingsley Temitope, Obinna Norman, Kennedy Odiong, da Stella Chukwuma.
Sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Binos Yaroe, ne ya gabatar da kudirin korar mambobin a ranar Talata yayin babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, inda wakilai suka amince da kudirin ta hanyar kada kuri’ar baki.
Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami
Da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar, sakataren tsare-tsare na ADC, Chinedu Idigo, ya zargi waɗanda aka kora da haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyar ta hanyar ƙirƙirar rarrabuwar kawuna.
