Yayin da ake cika shekaru 12 cif-cif da sace ƴan matan makarantar garin Chibok su 272 da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, masu fafutukar ganin an saki ƴan matan da ake kira da “BringBackOurGirls” suna neman amsa dangane da inda ragowar ƴan matan suke.
Aƙalla ƴan mata 187 ne aka ceto ko kuma suka tsere daga hannun waɗanda suka sace su, inda har yanzu ba a san makomar ƴan matan guda 83 ba.
Wannan ne ya sa ƙungiyar ta BringBackOurGirls ke neman sanin a halin da suke ciki.
A watan sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta zayyana wasu buƙatu da ta ce suna neman bayani a kansu ciki har da sanin halin da ragowar ƴan matan 83 suke ciki.
