Rundunar yansanda ta jihar Edo ta kama wasu gungun ɓatagari da su ka haɗa da jami’an ƴansanda biyar da gida ɗaya da aka kora daga aiki, tare da wasu mutum uku, bisa zargin cin zarafi, sace mutane da kuma kwace musu kudade a jihar.

Jami’an da aka kama sun hada da ASP Bonny Paul Onajite, Insifekta Ehubarieme Wisdom, Insifekta Arebame Godspower, Kofur Mordi Philip, Kofur Okon Elvis, da kuma Destiny Emmanuel wanda aka kora daga aikin dan sanda.

Rahoton Daily Trust ya ce sauran wadanda aka kama tare da jami’an sun hada da Goodluck Jaja, mai sana’ar POS, da Samuel Nicholas da Etim Bright, wadanda dukkansu direbobin karamar mota ne.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikioedem, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa kungiyar ta kama mutane ne ta hanyar karyar cewa su jami’an tsaro ne, inda suke sace su tare da kwace musu kudade a Benin City.

Ta kara da cewa jami’an da har yanzu suke bakin aiki suna fuskantar matakan ladabtarwa na cikin gida, ciki har da tsarewa kafin daga bisani a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

A cewarta, gungun ɓatagarin na gudanar da ayyukanta ne a yankin Teboga da ke kusa da Aduwawa, inda suke tilasta wa wadanda suka kama shiga motoci, su zagaya da su a cikin birni kafin a tilasta musu cire kudade ta hanyar POS cikin barazana.

Ta ce kamen ya biyo bayan korafe-korafe da dama daga mazauna yankin kan yadda wasu ke yin kame da kwace kuɗaɗe suna fakewa da sunan ’yan sanda.

Ikioedem ta bayyana lamarin a matsayin babbar barazana ga amincewar jama’a, tana mai cewa ayyukan waɗanda ake zargin sun jawo wa rundunar ’yan sanda ɓacin suna.

Ta kuma gargadi masu sana’ar POS da su guji taimakawa irin wadannan ayyuka na haram, tana mai cewa duk wanda aka samu da hannu a ciki zai fuskanci hukunci.

Sai dai ta bukaci wadanda suka fuskanci wannan abu su fito su bayar da bayanai domin taimakawa bincike, tana mai jaddada kudirin rundunar na tabbatar da gaskiya da adalci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version