Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Hajiya Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jihar ta dindindin.

Wannan na kunshe a wata samarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kano,. Mustapha Muhammad ya fitar,.inda ya ce gwamnan ya sanar da haka ne a wajen bikin biyan ƴan fansho hakkunan su, karo na shida.

Harin masu iƙirarin jihadi ‘ya kashe wani babban jami’in soja’ a jihar Borno

Ya ce tabbatar da Maimota a wannan lokacin ya yi daidai domin samun cigaba wajen gudanar da aikin gwamnati.

Inda ya ce an tabbatar da Maimota ne bayan ta rike matsayin na rikon kwarya lokacin da gwamnan ya cire Abdullahi Musa daga mukamin na shugaban ma’aikatan jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version