Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Jihar Kano, ta koka a kan sama da faɗi da ake yi da madarar tamowa ta ƙananan yara masu larurar rashin abinci mai gina jiki tare da handame jakunkunan ɗalibai da ke yankunan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar.

A bisa haka gwamnatin, ta gindaya doka da oda mai ƙarfi ga dukkan waɗanda suke da alhaki wajen karkatar da irin waɗannan muhimman kayayyakin tagomashin inganta rayuwar al’umar dake kafatanin jihar.

Jami’in Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa Reshen jihar Kano, Malam Balarabe Yusuf Sani, ya nuna damuwa bisa yadda rashin gaskiya da amana suka mamaye jama’a, musamman ganin yadda wasu iyaye ke iya sarayar da tallafi mai alfanu ga rayuwar ‘ya’yansu.

Haka kuma, ya ja hankalin guɓatattun ma’aikatan lafiya su kiyaye aiki cikin tsoron Allah, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta ruwaito.

“Yadda ake rabar da tamowa shi ne, ba kawai zuwa ake da yaro asibiti ana ba shi ba, sai an auna shi an tabbatar yana buƙatarta, sannan a ba shi. Kowace ƙaramar hukuma tana da santar da ake bayarwa; wata santarta ɗaya ne wata ya fi haka, ya dai daganta da yawan yara masu larurar cutar tamowa a kowane yankin.

Kuma duk sadda yakamata a dawo karɓar wa yaro, to a zo da shi ne a sake auna shi, idan nauyinsa ya ƙaru tabbas ana yi masa amfani da tamowar, idan kuma bai ƙaru ba, to alamu ne ana karkatar masa da ita kasuwa ko ana shanye masa!” Jami’in Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa Reshen jihar Kano, Malam Balarabe Yusuf Sani.

Daraktar Ayyuka na Musamman a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin-gida ta jihar Kano, Hajiya Halima Ahmad Ishaq, ta ja hankalin al’uma dangane da alkinta dukiya da kadarorin gwamnati domin amfanar kai-da-kai, sannan ta yi kira ga iyaye mata su kula da haƙƙoƙin ‘ya’yansu ta fuskar ilimi da tarbiya, musaman kiwon lafiyar yara masu larurar tamowa.

“Lallai ne a ja hankalin mutane, musamman mata, don Allah don Annabi su daina sayar da tamowar da ake bai wa ‘ya’yansu tallafi, ko shanye musu, ko su ƙyale iyaye maza su amshe, ko bai wa masu reno, ko kuma sayar wa mata masu ciki, wannan duk bai kamata ba!” Daraktar Ayyuka na Musamman a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin-gida ta jihar Kano Hajiya Halima Ahmad Ishaq.

A jawabin Shugaban Sashen Kula da Lafiya na Bichi, Malam Kabiru Abubakar Gwarzo, wanda Malam Isa Shitu ya wakilce shi, ya ba da tabbacin za su sa ido ga ma’aikatan lafiyar yankin wajen kawar da matsalar.

Kazalka, Sakataren Hakimin Bichi, Galadiman Kano Alhaji Mannir Sanusi, Malam Idris Shitu Malikawa da ya yi magana a madadinsa, ya ce, za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen fadakar da al’umar Ƙaramar Hukumar Bichi domin magance irin waɗannan matsaloli a yankin baki ɗaya.

Zaman ya haɗa da; wakilin Asusun Tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), Malam Yunusa Ahmad, wakilin Hakimin Bichi, jami’in Hukumar Wayar da Kan “Yan Kasa Reshen jihar Kano da wakilin sashen lafiya na yankin.

 

Blueprint

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version