Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba da umarnin kama shugaban tsagin jam’iyar PDP Tanimu Turaki.

Jaridun ƙasar sun ruwaito cewa mai shari’a Peter Kekemeke, ya ba da umarnin ne bayan da Turaki ya ƙi bayyana a gaban kotun, domin bayar da bahasi kan wani zargi da Babban Sufetan ƴansandan ƙasar ya shigar a kan sa.

A cikin ƙarar, rundunar ƴansandan ƙasar ta yi zargin cewa shugaban tsagin PDPn ya gabatar da bayanan ƙarya a wani ƙorafi da ya shigar a shekarar 2022.

Mai shari’a Kekemeke, ya ce babu wata hujja da Turaki ya bayar na ƙin bayyana a gaban kotun, duk da cewa an sanar da shi.

Kotun ta ba da umarnin a gabatar da shi a gaban kotun idan aka samu nasarar kama shi.

Turaki ya riƙe muƙamin ministan ayyuka na musamman a gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version