Ma’aikatar tsaron ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce mambobi biyu na rundunar sojin ƙasar sun mutu bayan da wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari sakamakon tangarɗar na’ura.

Har yanzu ba a tabbatar ko lamarin yana da alaƙa da rikicin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran ba.

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

Ma’aikatar tsaron ta ce mutanen biyu da suka mutu suna “cikin aiwatar da aikin ƙasa ne” a lokacin da hatsarin ya faru ranar Litinin.

Ta kuma bayyana cewa tana miƙa ta’aziyya da jaje ga iyalan waɗanda ta kira shahidai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version