Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, kwamared Aminu Abdulsalam, bisa zarge-zargen aikata manyan laifuka a kan aiki, wulaƙanta aiki da kuma karya dokokin aikin gwamnati.

Matakin ya biyo bayan wani ƙorafi da ɓangaren zartarwa ya gabatar wa majalisar, inda aka buƙaci ta ɗauki mataki a kan Abdulsalam kan wasu zarge-zargen da suka shafi yadda ya gudanar da aikinsa a lokacin da yake kwamishinan ƙananan hukumomi tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.

Gwamnatin Jigawa Ta Tsige Alƙalin Kotun Musulunci Kan Rashawa

Da yake karanta ƙorafin, Shugaban nasu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce sanarwar ta yi daidai da tanadin sashe na 188 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Ya bayyana cewa zarge-zargen sun shafi ayyukan Abdulsalam ne a lokacin da yake kula da ƙananan hukumomi 44 na jihar.

 

Ƙorafin ya ƙunshi zarge-zarge kamar haka: Cin amanar al’umma da keta haddin aiki.

 

Ana zargin Abdulsalam da karkatar da kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi domin amfanin kansa. Daga watan Yuni 2023 zuwa Janairu 2024, ana zargin ya karɓi kuɗaɗen cin hanci har naira miliyan ₦462 a cikin watanni bakwai.

 

Karkatar da Kuɗaɗe da amfani da muƙami ta hanyar da ba ta dace ba: Daga watan Fabrairu 2024 zuwa Yuli 2024, an ce ya karɓi kimanin Miliyan ₦726 daga ƙananan hukumomi da sunan aiwatar da wasu ayyuka na musamman.

 

Amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba:

 

Ana kuma zargin Abdulsalam da taimakawa wajen sakin kuɗi har ₦440 miliyan ga kamfanin North Med Pharmaceutical Limited, wanda ake cewa ya saɓa dokokin sayen kayayyakin gwamnati da kuma ƙa’idojin kashe kuɗin jihar.

 

Babban laifi a kan aiki:

 

An ce waɗannan ayyuka sun kai matsayin manyan laifuka a kan aiki kamar yadda sashe na 188(2) na kundin tsarin mulki ya tanada, domin suna nuna karya dokokin tsarin mulki da ƙa’idojin da suka shafi masu riƙe da muƙaman gwamnati.

 

Dala ya bayyana cewa bisa hujjojin da aka gabatar, ya kamata a tsige mataimakin gwamnan tare da cire shi daga muƙaminsa bisa tsarin da kundin tsarin mulki ya tanada.

 

Sai dai an bai wa Abdulsalam wa’adin makonni biyu domin ya mayar da martani kan zarge-zargen da ke ƙunshe cikin ƙorafin.

 

Rahotanni na nuni da cewa batun ƙin canja jam’iyya daga NNPP zuwa APC shi ma yana daga cikin dalilan da ake kawowa na yunƙurin tsige mataimakin gwamna, ko a kwanakin baya an dinga yaɗa wa cewa majalisar za ta tsige shi, wanda a wancan lokacin majalisar dokoki ta musanta zargin, wanda a yau kuma sai ga batun tsigewar ya fito.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version